An sace baban Mikel Obi

Mikel Obi
Image caption Mikel Obi

Rahotanni daga Nijeriya na cewa wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun sace mahaifin dan wasan nan na Chealsea, John Mikel Obi, a Jos babban birnin jIhar Filato. Rahotannin dai sun bayyana cewa na sace mahaifin dan wasan ne yayin da yake komawa gida daga wajen aiki a ranar Juma'a da ta gabata.

John Mikel Obi, ya yi kiran da a taimaka ma shi wajen gaano mahafinsa, wanda aka yi imanin cewa an yi garkuwa da shi.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake sace dangin wani dan wasan Najeria dake buga kwallo a Ingila ba. A shekara ta 2008, wasu 'yan bindiga sun sace yayan Joseph Yobo, tsohon mai tsaron baya na Everton, amma daga bisani aka sako shi.