Wani babban dan siyasar Zimbabwe ya rasu

Solomon Mujuru Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Solomon Mujuru

Jami'ai a kasar Zimbabwe sun ce daya daga cikin shahararrun 'yan siyasar kasar Solomon Mujuru ya rasu bayan da wuta ta tashi a gidan gonar sa.

Mr. Mujuru dai ya kasance mataimakin shugaban 'yan yakin sunkurun da suka dora shugaba Robert Mugabe a kan mulki a shekarar 1980, kuma yana daya daga cikin wadanda suka tabbatar da karbar iko.

Matar sa Joice Mujuru ta taba rike mukamin mataimakiyar shugaban kasar har sau biyu.

kafun rasuwar sa, Mr. Mujuru na tattaunawa da karamar jam'iyyar kawancen gwamnatin kasar wato Movement for Democratic Change.

Jim kadan bayan gobarar ta tashi, ministan tsaron kasar Sydeny Sekeramai ya ziyarci gidan gonar da ke Beatrice, kimanin kilomita tamaninin a kudancin birnin Harare da sanyin safiyar ranar Talatar.

Ya kuma ce: "Yanayi ne mai wuya. Mun zo nan da sassafe bayan an shaida mana abin da ya faru. Da farko ba mu yarda ba, amma ya kone ne kurmus".

Jami'an 'yan sanda na binciken musabbabin gobarar, wacce ta lashe gidan gonar.

Janar Mujuru mutum ne mai tsare-tsare da kuma karfin fada a ji a jam'iyyar Zanu PF ta shugaba Mugabe.

A lokacin yakin da aka yi da Rhodesia a shekarun alif dari tara da saba'in, Mujuru ne ya jagoranci mayakan da suka yi gwagwarmaya da makamai, tare da marigayi Josiah Tongogora, yakin da ya kawo Robert Mugabe bisa karagar mulki.

A lokacin da aka samu 'yancin kai, Mujuru ya karbi ragamar shugabancin sojojin kasar.

Shekaru goma bayan nan ya yi ritaya inda ya shiga harkar kasuwanci.