Dakarun Syria sun kai hari akan Latakia

Masu zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Mummunan ruwan bama baman da sojojin gwamnatin Syria suka yi a kan birnin Latakia na gabar ruwa, ya tilastawa dubun dubatar 'yan gudun hijirar Palesdinawa tserewa daga sansanin da suke zaune.

Wani kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya ce an kashe akalla Palesdinawa hudu, kuma rahotanni sun ce wasu karin da dama sun samu raunika.

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce har yanzu ba'a amsa kiran da ta yi ba, na samun izinin shiga sansani don kai kayan agaji ga 'yan gudun hijirar.

Rahotanni sun ce harin da ake kaiwa Latakia , wanda ya shiga rana ta ukku a jere, ya yi sanadiyyar hallaka akalla mutane talatin da tara.