'Akwai masu tsattsauran ra'ayin Islama a 'yan tawayen Libya'

Image caption Liam Fox

Sakataren Tsaron Burtaniya Liam Fox ya ce akwai masu tsatsauran ra'ayin Islama a cikin 'yan tawayen kasar Libya.

Ya kara da cewa don haka dole ne a ware masu irin wannan ra'ayi a yayin da kasar ke tunkarar tsarin mulkin dimokradiyya.

A makon jiya ne shugabannin 'yan tawayen suka bayyana cewa wasu mayaka daga cikinsu da ke da tsatsauran ra'ayin Islama ne suka kashe kwamandan sojojin 'yan tawayen, Janar Abdel Fattah Younes.

Mista Fox ya shaidawa BBC cewa har yanzu ba a tabbatar da wadanda suka yi kisan ba, wanda aka yi kwana guda bayan da Burtaniya ta amince da majalisar 'yan tawayen a matsayin halattacciyar gwamnatin Libya.