Direbobin bas-bas na yajin aiki a Kaduna

Taswirar Nijeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Nijeriya

A Nijeria direbobin bas-bas sun fara wani yajin aiki gama-gari a Kaduna domin nuna damuwa a bisa abinda suka ce cin zarafi daga jamian tsaro ke yi musu.

Direbobin na zargin jami'an tsaro da lakada musu duka da fasa musu motoci a bisa batun ajiye motocin su a bakin hanya.

A yau din dai jama'a da dama sun yi ta taka sayyada don rashin abubuwan hawa.

Gwamnatin jihar dai a yanzu na tattaunawa da jami'an yan sanda, sojoji da masu yajin aikin domin lalumo hanyoyin warware matsalar.