An hana wasu jami'an gwamnati fita daga Nijer

Shugaban Nijer Muhammadou Issoufou
Image caption Shugaban Nijer Muhammadou Issoufou

Rahotanni daga jamhuriyar Nijer sun ce an hana wasu manyan jami'an gwamnati a kasar fita kasashen ketare.

Rahotannin suka ce hakan ya sa an dakatar da wani dan majalisar dokokin kasar daga tsallaka kan iyaka, inda aka shaida masa cewa sunansa yana cikin wadanda ake bincike akansu.

Wannan dalili ya sa majalisar dokoki ta jamhuriyar Nijer din ta ce za ta tattauna kan wannan lamari.