Tankokin yakin Syria sun yi ruwan harsasai a kan garin Hama

Hakkin mallakar hoto Reuters

Ana ci gaba da ruwan harsasai a birnin Hama na kasar Syria.

Masu fafutukar kare hakkin dan adam sun ce akalla mutane hudu ne aka kashe yayin da dakarun gwamnati suka kai hari da tankunan yaki daga wajen garin.

Jama'a da dama ne aka bada rahotan kashewa ranar Lahadi, yayin da dakarun tsaro suka kai hari kan masu zanga zanga.

Wakilin BBC ya ce harin da aka kai a Hama ranar Lahadi shi ne mafi muni tun bayan da aka fara rikici watanni hudu da rabin da suka wuce a kasar Syria.

Nan gaba a yau ne kwamitin tsaro na MDD zai wata ganawa a asirce a New York ga me da batun na Syria.