Rasha ta nuna damuwa kan rikicin da ake yi a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rasha ta nuna matukar damuwa akan rohotannin tashin hankalin da ke fitowa daga garin Hama a Syria, inda aka ce dakarun tsaro sun kashe wasu fararen hula.

Ma'aikatar harkokin wajen Rashan ta ce yin amfani da karfi akan fararen hula da kuma wakilan ba abu ne da za'a amince da shi ba, kuma dole ne a daina.

Amma kuma har ya zuwa safiyar yau, an samu rohotannain tashin hankali, inda fararen hula ke cewa tankuna sun yi ta harba rokoki akan garin na Hama, kuma har mutane Hudu sun mutu.