Rikicin bashin Amruka: Majalisar dattijai za ta kada kuri'a

Shugaban Amruka Barack Obama Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Amruka Barack Obama

Majalisar dattijan Amurka za ta kada kuri'a akan kudirin dokar amincewa da yawan bashin da kasar zata iya ciyowa.

Gwamnatin Shugaba Obama ta ce zata iya cimma yawan bashin da zata iya karba, a bisa doka, kafun karshen wunin yau.

Idan har majalisa ba ta amince da kudirin dokar ba, to gwamnati ba za ta iya gudanar da wasu harkokinta ba ta fuskar kudi, kuma zata gaza biyan bashin da ake bin ta.