An sabunta: 26 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 19:19 GMT

Sauyi a kasashen Larabawa

An saki 'yar jaridar BBC da aka kama a Masar

Shimaa Khalil

Shaimaa na daga cikin masu hada shirye-shirye na BBC a Masar

An saki daya daga cikin masu hada shirye-shirye na BBC Shaimaa Khalil, wacce aka kama a dandalin Tahrir a birnin Alkahira na kasar Masar.

Babbu wani dalili na kamen da ak yi mata a ranar Litinin, sai dai ya zo ne jim kadan bayan da 'yan sanda da sojoji suka tarwatsa masu zanga-zanga da suka shafe makonni uku a can.

An tsare ta na tsawon sa'o'i 20 a wani sansanin soji, sannan aka kaita ofishin mai gabatar da kara na soji kafin daga bisani a sake ta.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce an daki masu zanga-zangar sannan aka fasa wayoyinsu na salula.

Wakilin BBC ya ce kamar yadda masu fafutukar kare hakkin bil adama suka fa di Shimaa na daya daga cikin mutane tamanin da biyun da aka kama ranar Litinin da daddare a dandalin Tahirir, ciki harda 'yan jaridar kasar ta Masar da dama.

Suka kara da cewa an nufi duk wanda ya yi kokarin daukar hoto.

Tun da farko BBC ta nemi da a gaggauta sakin Ms Shimaa.

"Mun damu matuka kan tsare Shaimaa Khalil. Kwararriyar 'yar jarida ce, da ke aikinta cikin ruwan sanyi. Muna yin duk abinda ya kamata domin ganin an sake ta," a cewar wata sanarwa da BBC ta fitar.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.