Gwamnati ta sauya ra'ayi kan tattaunawa da Boko Haram

Boko Haram
Image caption Kungiyar na kai hare-hare da dama a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce kwamitin da ta nada ba zai tattauna da kungiyar Boko Haram ba kamar yadda aka fada da farko - za su yi sharar fage ne da tattara shawarwari kan yadda za a samu zaman lafiya a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Sakataren gwamnatin Tarayya Anyim Pius Anyim, ya bayyana hakan a wajen rantsar da mambobin kwamitin na mutum bakwai, amma bai yi karin haske kan sauya manufar da aka samu wurin tunkarar kungiyar ba.

A baya, ofishinsa ya bayar da sanarwar a karshen mako yana mai cewa aikin kwamitin "zai hada da shiga tsakanin gwamnatin tarayya....da Boko Haram sannan su fara tattaunawa da kungiyar."

"Wannan ba kwamitin sulhu ba ne," a cewarsa. "Kwamiti ne da zai yi bincike. Ya kuma bada shawara."

Sai dai ya ce a karshen aikinsa, kwamitin zai iya bada shawara kan a tattauna da kungiyar.

An bukaci su gabatar da sakamakon bincikensu kafin ko kuma a ranar 16 ga watan Agusta.

Kwamitin ya kunshi ministan kwadago da na tsaro da kuma na birnin tarayya Abuja.

An dade ana batun ko gwamnatin za ta tattauna da 'ya'yan kungiyar ko kuma a'a, inda jami'ai ke kaffa-kaffa da batun.

Wasu dai na ganin kamata ya yi a baiwa 'ya'yan kungiyar makamanciyar afuwar da aka baiwa masu fafutukar yankin Niger Delta.

Birnin Maiduguri a yankin Arewa maso Gabashin kasar na fuskantar hare-hare ba kakkautawa a 'yan makwannin nan wadanda kuma ake alakantawa da kungiyar ta Boko Haram.

Ita dai kungiyar na ikirarin kafa tsarin shari'ar musulunci ne a wasu jihohin kasar, sai dai jama'a da dama a yankin ba sa goyon bayan hanyoyin da take bi wajen cimma burin na ta.