Boko Haram: Gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamitin nemo bayanai

Hakkin mallakar hoto System
Image caption Bangaren taswirar Nijeriya

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta kaddamar da wani kwamiti wanda aka dorawa alhakin gano yadda za a fuskanci rikicin da ake yi da kungiyar Jama'atu Ahlussuna lidda'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram. An kafa kwamitin ne bisa jagorancin Ambasada Usman Gaji Galtimari. Sai dai kafa kwamitin ke da wuya shugaban kwamitin ya ce lokaci yayi kadan, sannan ana bukatar kara fadada mambobin da ke ciki. Sakataren gwamnatin Tarayyar Nijeriya, Anyim Pius Anyim ya ce aikin kwamitin na tattaro bayanai ne ba na sasantawa ba.