An cinma matsaya da ma'aikatan Nijeriya

A Najeriya, gwamnatin tarayya da kungiyar kwadagon kasar sun cimma yarjejeniya a kan biyan sabon albashi mafi karanci na naira dubu goma sha takwas.

A yanzu dai gwamnati ta amince za ta biya sabon albashin ta yadda zai shafi dukkan ma`aikata, sabanin yadda ta cije a baya cewa sai matakin albashi na daya zuwa na shidda ne kadai za su ci gajiyar sabon albashin.

Kungiyar kwadagon ta ce zata tattauna kan wannan batu a gobe, kafin ta bayyana matsayinta.