Rashin aikin yi tsakanin matasa

Funmi Wale-Adegbite
Image caption Funmi Wale-Adegbite na ganin lamarin na da alaka da al'ada

Rashin aikin yi ga matasa na daga cikin matsalolin da ke addabar kasashe da dama, sai dai masana na ganin a Najeriya shagwaba yara da iyaye ke yi na kara ruruta matsalar.

Funmi Wale-Adegbite, wacce ke aikin daukar ma'aikata a Legas, ta shaida wa BBC cewa shagwaba yara da iyaye ke yi na daga cikin manyan matsaloli a Najeriya.

A Najeriya muna da matasan da basu da aikin yi daga shekara 15-24 - ina ganin yawansu zai haura kashi 30 cikin dari.

Shagwaba a ra'ayina na daga cikin manyan abubuwan da ke tauye yara. Iyaye sukan nuna kauna fiye da kima ga 'ya'yansu.

Talaka da mai kudi a Najeriya, kowannensu ana saran ya dauki nauyin yaransa har lokaci mai tsawo.

Al'adarmu ta tanadi kula da yara tun suna kanana har girmansu.

Iyaye kan baiwa 'ya'yansu kudaden kashewa - wani lokacin har bayan sun kai shekaru talatin.

Shi ya sa za ka ga wani saurayin na nuna halayya irinta yara.

A Burtaniya, dan shekara 18 ya riga ya zama babba, amma a Najeriya yaro ne karami.

Kowa na son ya samu

Yawancin mutane kan kammala jami'a suna 'yan shekaru 27, kuma ba abin mamaki ba ne ka ga dan shekara 27 wanda bai taba yin aiki ba, koda kuwa dan talaka ne.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wai shin matsa a Najeriya na bukatar abubuwa da yawa?

Yawancin matsalar na tattare ne da wadanda suka kammala digiri a matakin farko; ba su da wata alkibla ko kadan.

Iyaye da dama kan kwallafa rai sai 'ya'yansu sun samu babban aiki kamar na banki ko kamfanonin sadarwa ko na mai.

Jama'a ba sa tsayawa su koyi aiki yadda ya kamata - su dai kawai su samu kudi.

Kusan kashi 70 cikin dari na da wannan tunanin, kuma iyayensu na taka rawa wajen hakan.

Sun gwammace su yi aikin shara a manyan kamfanoni na duniya, maimakon aiki a matsayin mai digiri a wani kamfanin da bai yi suna ba.

Dalibai sun rasa 'dama'

Lokacin da iyaye na suke shekaru 18, babu damarmaki kamar yanzu, suna zaune ne a kauyuka, babu intanet, ba wayar salula, kuma ba su da iyayen da za su tallafa musu.

Amma matasan yanzu ba su da kwazon neman na kansu.

Sai dai akwai matsala a jami'o'in Najeriya; ta yadda ba a shirya daliban domin fuskantar aiki, kawai ana ba su digiri ne.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A cewar Funmi, dalibai ba sa samun yadda ya kamata a jami'a

Lokacin da nake karatu a Burtaniya, muna da ofishi na musamman da ke wayar da kan dalibai, tun aji biyu za ka fara samun aikin da za ka rinka yi wanda ke da alaka da abin da kake karantawa.

Amma lamarin ba haka ya ke ba a Najeriya, ba wani tallafi na wayar da kai da ake yi wa dalibai.

'Ba abinda ke zuwa cikin sauki'

Akwai bangarori da dama da ke bukatar tallafi a Najeriya. Alal misali koyarwa - da dama ba sa son yaransu su yi aikin koyarwa. Don haka akwai karanci a wannan bangare.

Na tattauna da wata yarinya, wacce na baiwa shawarar cewa za ta dace da koyarwa a kananan makarantu.

Amma sai tace min: "Kada ki bari iyaye na su ji labari saboda sun fi so na yi aiki a banki."

Abu ne da yake da alaka da al'ada don haka yana da wuya a iya sauya shi.