Kasashen duniya na kara sa matsin lamba kan Syria

Masu zanga-zangar na matukar nuna adawa da shugaba Asad Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zangar na matukar nuna adawa da shugaba Asad

A karan farko, sakatariyar kula da harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta gana da 'yan adawar kasar Syria.

'Yan adawar wadanda ke zaune a Amurka sun ce sun yi amfani da damar ganawar da sukai da ma'aikatar harkokin wajen dan su nemi Amurka tai kira ga shugaban kasar Syria, Bashar al Assad da ya sauka daga mulki ba tare da wata wata ba.

Taron yazo a daidai lokacin da gwamnatin Syria ke fuskantar matsin lambar diplomasiyya na ta dakatar da hare haran da take kaiwa garin Hama, inda aka ce an kashe kimanin mutane dari da arba'in a yan kwanakinnan.

Kwamitin tsaro na MDD ya shiga kwana na biyu a taron da suke kan Syrian, yayin da kasar Italia ta dawo da jakadanta daga Damascus, sannan kuma ana samun karin wasu jami'an gwamnatin Syria da kungiyar tarayyar Turai ke sawa takunkumi. Micheal Mann kakakin Jami'ar kula da harkokin waje ta kungiyar tarayyar Turai ya ce, muna sa matsin lambar siyasa da yawa kan gwamnatin wadanda ke tasiri kai tsaye kan wadanda suka jawo rikicin.

Rahotanni daga Hama sun ce ana ci gaba da gumurzu tsakanin dakarun gwamnatin Syria da masu zanga zanga, inda masu fafutukar kare hakkin dan adam ke cewa an kashe karin wasu mutane da tankokin yaki da kuma mutanan dake buya suna harbi.

Dakarun gwamnati na kokarin yiwa birnin kofar rago, amma dai ba su kai ga shiga can ciki ba. Wakilin BBC a yankin gabas ta tsakiya ya ce halin da ake ciki kowa ya ja daga, amma galibin Hama din na hanun mazauna birnin.

Wakilin BBC ya ce da alama dakarun gwamnatin basa san yiwa birnin dirar mikiya su kwace shi a lokaci daya amma dai suna yi ne sannu a hankali.