Kotu ta amince Al Mustapha ya nuna mata faifan Bidiyo

Manjo Hamza Al Mustapha
Image caption An shafe shekaru ana wannan shari'a

Babbar kotun jihar Lagos ta ci gaba da sauraren ba'asin tsohon mai tsaron lafiyar marigaryi Janar Sani Abacha, watau Manjo Hamza Al-Mustapha.

Kotun ta kuma amince masa ya nuna faifan bidiyon da yayi zargin suna kunshe da hotunan wasu manyan mutanen yankin kudu maso yammacin Nigeria da yayi zargin sun karbi toshiyar baki dan a manta da yadda ya ce an hallaka Chief MKO Abiola .

A zaman kotun ,Manjo Hamza Almustapha,ya ambachi sunayen wasu fitattun shugabannin kabilar Yarbawa da yake zargin suna cikin wadanda suka karbi wannan toshiyar baki bayan mutuwar MKO Abiola.