Yau Nijer ta cika shekaru 51 da samun 'yancin kai

isoufou
Image caption Shugaban Nijer Mahamadou Issoufou

Shugaban kasar Nijar ya sanar da cewa an kama mutane goma dangane da abin da ya ce wani yunkuri ne na juyin mulki kwanan nan.

Da ya ke jawabi ranar jajibirin cikar kasar shekaru hamsin da daya da samun mulkin kai, Shugaba Mahamadou Issoufou ya ce wasu daga cikin mutanen da ke tsare jami'an soji ne yayin da daya daga cikinsu ya ranta a na kare.

Wakilin BBC a Yamai Iddy Baraou ya ce wannan ne karo na farko da gwamnatin kasar ta fito ta yi magana a kan wannan juyin mulkin da ake zargin an yi yunkurin aiwatarwa:

A watan Maris ne dai aka zabi Mahamadou Issoufou bayan wani juyin mulki wanda ya kifar da gwamnati tsohon shugaban kasa, Mamadou Tandja.