Motar bas ta kashe mutane 14 a Lokoja

Motar bas ta kashe mutane 14 a Lokoja
Image caption Irin wannan hadari da fashi da makami ba baki ba ne a Najeriya

Rahotanni a Najeriya sun ce a kalla mutane 14 ne suka hallaka bayan da wata motar Bas ta tattake wasu mutane da 'yan fashi suka kwantar akan hanya domin yi musu fashi.

"Mutane 14 ne suka mutu yayin da dama suka samu jikkata," kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Kogi ASP Ajayi, ya tabbatarwa da BBC. Lamarin dai ya faru ne a kan hanyar Lokoja zuwa Okene a jihar Kogi.

Motar dai na tafiya ne daga garin Lokojo da ke tsakiyar kasar zuwa babban birnin tarayya Abuja.

"Jami'an tsaro na iya kokarinsu, ko a lokacin da abin ya faruma, jami'an na can suna bata kashi da wasu 'yan fashin daban a jeji.

'muna kokarin ganin karshen lamarin'

"Ba zai yi wu ace muna kan titi kuma muna cikin daji a lokaci guda ba. Amma ina tabbatar da cewa muna kokarin ganin karshen lamarin," a cewar Ajayi.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da 'yan fashi da makami suka kwantar da jama'a a wani bangaren titin domin yi musu fashi.

Ana cikin haka ne kuma sai wata motar Bus ta tawo inda 'yan fashin suka tsayar da ita, amma direban ya ki tsayawa abinda kuma yasa shi bi takan mutanen da aka kwantar a kasan inda ya tattakesu - ita wata motar daukar kaya da ke bin Bus din ta kara bi ta kan mutane inda nan take mutane 14 daga ciki suka rasa rayukansu.

Jami'an 'yan sanda sun ce babu wanda suka kama daga cikin 'yan fashin domin sun riga sun tsere kafin su isa wurin.

Mai yiwuwa adaddin wadanda suka mutun ka iya karuwa ganin cewa akwai da dama da suka munanan raunuka.

Afkuwar irin wadannan hadri dai da kuma fashi da makami, ba wani bakon abu bane a kan hanyoyin Najeriyar, abinda a mafi yawan lokuta a ke alakantawa da rashin kyawun hanyoyi da kuma tsaro.