Mubarak ya musanta tuhumar da ake yi masa

Tsohon Shugaba Hosni Mubarak na Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsohon Shugaba Hosni Mubarak na Masar

Hambararran shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak da 'ya 'yansa biyu sun musanta aikata laifukan da ake tuhumarsu, a bayyanarsu ta farko a kotu dake birnin Alkahira, inda ake tuhumarsu da laifukan cin hanci da kuma bada umarnin kashe daruruwan masu zanga zanga.

Tsohon Shugaba Mubarak mai shekaru tamanin da uku ya yi korafin rashin koshin lafiya, ya kuma kasance kan gadan asibiti baki dayan tsawon lokacin zaman kotun na yau inda aka sa shi cikin wani keji a cikin kotun.

An nuna yadda shari'ar ta gudana a wani katan majigi a wajen kotun, inda fada ya kaure tsakanin magoya bayan Mr Mubarak da wadanda basa san shi.

Yanzu haka an dage shari'ar har zuwa tsakiyar wannan watan domin ci gaba da ita.

Tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak ya kasance na farko cikin shugabannin kasashen gabas ta tsakiya na wannan zamani da mutanansa suka gurfanar a gadan kuliya.

Ga mutanen Masar dama, shari'ar ta ba da damar cewa, za ayi adalci, bayan kwashe kimanin shekaru talatin na mulkin da ake gallazawa 'yan adawa, da hana ruwa gudu a harkokin siyasa da cin hanci da kuma yadda talauci ya yiwa jama'a katutu.

Sai dai kuma wasu na kallon Mr Mubarak a matsayin wata alama ta zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A watan Fabreru ne aka hambarar da Mr Mubarak lokacin da akai ta yin zanga zanga a kasar.