Mata na taron neman zaman lafiya a Kaduna

Hakkin mallakar hoto System
Image caption Taswirar Nijeriya

A jihar Kaduna ta Nijeriya wata kungiyar mata ta hada kai tsakanin Musulmi da Kirista ta fara wani taro na kwanaki uku domin tattaunawa da matan jihar kan yadda za a kawo karshen rikice rikice, takaddama da rashin kwanciyar hankali, domin samun ci gaban kasa da habakar tattalin arziki. Matan dake halartar wannan taro dai na ganin da dama daga cikin matsalolin dake afkuwa yayin kowanne irin rikici na karewa ne akan mata. Tun dai da aka tafka rikicin bayan zaben shugaban kasa ne wasu ke ganin ya kamata ayi wa tufkar rikice-rikice hanci a Nijeriya.