Yau Mubarak zai gurfana gaban kotu a Masar

mubrak
Image caption Tsohon shugaban MasarHosni Mubarak

Nan gaba a yau ne ake sa ran tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak, zai gurfana a gaban kotu a birnin Alkahira, inda ake tuhumarsa da aikata almundahana da kuma ba da umarni a kashe daruruwan masu zanga-zanga.

Ana sa ran Mista Mubarak, wanda boren da al'ummar kasar suka yi ya raba da mulki a watan Fabrairu, zai bayyana a gaban kotun shi da 'ya'yansa maza, da kuma wani tsohon ministan harkokin cikin gida.

Misrawa da dama na nuna shakku a kan ko Mista Mubarak zai bayyana don amsa tuhume-tuhumen da ake masa yayinda lauyansa ke ikirarin cewa yana fama da rashin lafiya mai tsanani.

An tsare tsohon shugaban na Masar a wurin shakatawar Sharm el Shaikh da ke gabar bahar maliya tun bayan kama shi watanni da dama da suka gabata.

An tsaurara matakan tsaro a Alkahira, inda 'yan sanda kusan dubu uku ke tsaron kotun.