Kamfanin mai na Shell ya dau alhakin bata muhalli a Naija-Delta

Yankin Naija Delta Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yankin Naija Delta

Kamfanin mai na Shell ya amince da cewa shi ne ke da alhakin kwararar mai manya-manya guda biyu a yankin Naija Delta.

BBC ta ga wata wasika daga kamfanin Shell din inda kamfanin ya amince da daukar nauyin wannan kwarar mai. Lauyoyin mutanen garin Bodo, wadanda ke zaune a cikin surkuki wanda ke malale da danyen mai sun ce wannan batu zai jawowa kamfanin mai na Shell biyan diyya ta miliyoyin daloli.

Lauyan mutanen garin na Bodo, Martyn Day ya ce wannan zai dasa dan-ba kan sauran kamfanonin da ke hakar mai a Birtaniya.