An jibge tankuna a tsakiyar birnin Hama na Syria

An jibge tankuna a tsakiyar birnin Hama na Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kusan mako guda kenan ana bata kashi a garin

Rahotanni daga Syria sun ce an jibge tankunan yaki a wani dandali dake tsakiyar birnin Hama.

Rahotannin sun ambato mazauna birnin na cewa tankunan yakin sun shiga dandalin Orantes bayan luguden wutar da suka yi ta yi.

Tun da farko wata kungiyar kare hakkin bil adama a Syria wadda ke nan London ta ce duk layukan tarho a Hama sun katse bayan da aka ji fashewar wasu bama bamai a birnin.

Osama wanda mazaunin Hama ne ya kwatanta halin da garin ke ciki.

Ya ce, yau da misalin karfe biyar na safe, dukan hanyoyin sadarwa da layukan waya da yanar gizo gaba daya su ka katse, can sai muka fara jin karar harbe harbe da tashin bama-bamai ta kowane bangare a birnin.

Yanzu haka kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya na ci gaba da tattaunawa a asirce game da yadda za'a tunkari rikicin na Syria.