Burtaniya ta nuna damuwa kan faifan bidiyo

Sakataren harkokin wajen Burtaniya
Image caption Ma'aikatar harkokin wajen Burtaniya ta nemi a yi taka-tsan-tsan

Ma'aikatar harkokin wajen Burtaniya ta ce tana kokarin tantance sahihanci wani faifan bidiyo da ya nuna wasu mutane 'yan kasashen waje su 2 da ake garkuwa dasu a Najeriya tun a watan Mayu.

Faifan bidiyon da aka aikewa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya nuna mutanen na cewa 'yan kungiyar Al-Qaida reshen arewacin kasar ne suka sace su.

A lokacin da aka sace mutanen a garin Birnin Kebbi dake arewacin Najeriyar dai hukumomi a kasar sun bayyana cewa, daya daga cikin mutanen dan kasar Burtaniya ne yayin da daya kuma dan asalin kasar Italiya.

Faifan bidiyon da kungiyar ta aikewa kamfanin dillancin labaru na Faransa AFP, ya nuna mutanen biyu sun bayyana cewa 'yan kungiyar A-Qaida ne ke garkuwa da su.

Inda dukkanin mutanen da aka sace suka karanta wata takarda da aka basu, suna rokon gwamnatocin kasashen su dasu biya bukatun wadanda suka yi garkuwa dasu, koda yake basu bayyana takamaiman bukatar da mutanen ke nema ba.

Sai dai a wata sanarwa, ofishin harkokin wajen Burtaniya ya bayyana takaicinsa game da faifan bidiyon, inda yace yana kokari a cikin gaggawa na tantance sahihanci faifan bidiyon da aka fitar na tsawon minti daya.

Italiya ma haka....

Ita ma a nata bangaren, ma'aikatar harkokin wajen kasar Italiya, ta bayyana cewa akwai bukatar a yi taka tsan-tsan inda tace tana aiki da takwararta ta Burtaniya da hukumomin Najeriya wajen tabbatar da sahihanci faifan bidiyon.

Tun a ranar 12 ga watan Mayun da ya gabata ne dai wasu mutane dauke da bindigogi suka sace mutanen biyu a masaukinsu a birnin Kebbi da ke arewacin Najeriya.

Rahotanni sun ce mutanen injiniyoyi ne dake aiki da kamfanin B Stabilini na kasar Italiya dake aikace-aikacen gine-gine.

Matukar dai aka tabbatar da sahihanci faifan bidiyon, zai kasance shi ne karon farko da reshen kungiyar Al- Qaida dake yankin arewacin Afrika ke sace mutane a Najeriya, kasar dake cikin kasashen duniya dake da dimbin albarkatun man fetur.

Reshen Kungiyar Al- Qaida dake yankin arewacin Afrika ya sha yin garkuwa da 'yan wasu kasashen waje a lokuta da dama, wadanda akasarinsu akan sake su bayan an biya kudaden fansa kamar yadda wasu rahotanni da ba'a tantance su ba ke cewa.