Japan zata kori mutane uku saboda nukiliya

nuclear Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tashar Nukiliya a Japan

Ministan cinikayya da masana'antu na Japan, Banri Kaieda, ya ce za a kori manyan jami'ai uku masu kula da manufofin makamshin nukiliya na kasar saboda ci gaba da fusknatr matsalar da ake yi a tashar nukiliya ta Fukushima.

A cewar mutanen da za a kora din su ne shugabannin hukumar kiyaye hadurran nukiliya da hukumar kula da albarkatun kasa da makamashi da kuma mataimakin minista mai kula da al'amuran tattalin arziki da cinikayya da masana'antu.

Wadannan ne dai jami'ai mafiya girman mukami da aka sallama a kan mtsalar ta tashar Fukushima.

Wakilin BBC Roland Buerk a Tokyo ya ce " gwamnatin Japan na shirin yin gagarumin garambawul ga yadda ake sa ido a kan harkar makamshin nukiliya a daidai lokacin da ake nuna damuwa cewa jami'an gwamnati na dasawa fiye da kima da masana'atun nukiliya".

Kusan watanni biyar bayan girgizar kasa da kuma guguwar Tsunami, har yanzu maaikata na kokarin magance matsalolin dake faruwa a tsahar nukiliya ta Fukushima.

A wannan makon an samu tururin da yafi kowanne a tashar nukiliyar, kuma a yanzu gwamnati zata kori manyan maaikata uku masu lura da tsarin nukiliyarta.