Zaa binciki sabuwar shugabar IMF

Christine Lagarde Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Christine Lagarde

Wata kotu a Faransa ta bada umarnin gudanar da bincike akan Shugabar hukumar bada lamani ta Duniya, Christine Lagarde, akan zargin cewa ta yi amfani da mukanin ta ta hanyar da bata dace ba, lokacin da take ministar Kudi a Faransa.

Ana zargin ta ne da amincewa da a biya diyya dala miliyan 400 a shekarar 2008 ga wani hamshakin attajiri, watanni bayan ya sauya sheka ya goyi bayan shugaba Sarkozy a lokacin da yake yakin neman zaben shugaban kasa.

Christine Lagarde dai ta ce babu wani laifinda ta aikata.

Wakilin BBC ya ce hukumar bada lamuni ta Duniya ta yi kokarin kaucewa irin abun kunyan da ya faru da tsohon shugabanta, Dominique Staruss Khan, kuma don haka ta ke nema ta tsaurara ka'dojin aikin sabuwar shugabar.