Gwamnatin Libya ta yi ikirarin samun nasara

Yakin Libya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yakin Libya

Gwamnatin Libya ta ce yanzu ta karbe iko da garin Zlitan dake yammacin kasar.

Ranar laraba da ta wuce, dakarun gwamnati sun ce sun kaddamar da wani babban hari akan 'yan tawayen dake garin, amma 'yan jaridan da aka kora daga garin sun ce babu wata alamar masu tada kayar baya.

Mazauna garin sun ce sun nuna wa 'yan jarida wani gida da suka ce wani harin da dakarun NATO suka kai ta sama ne ya ragargaza shi.

NATO dai ta ce tana bincike akan lamarin