Za a bada rahoto akan lalata muhali a Naija Delta

oil Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yankin Naija Delta a Najeriya

A yau Alhamis ne ake sa ran hukumar kula da muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya za ta wallafa rahoton wani bincike a kan yadda kwarar mai ta shafi Ogoni da ke yankin Naija Delta a Najeriya.

An dai kwashe shekaru biyu ana hada rahoton wanda ya jawo kace-nace saboda kamfanin mai na Shell ne ya samar da kudin binciken.

A ranar Laraba ne dai kamfanin mai na Shell ya amince da cewa shi ne ke da alhakin kwararar mai manya-manya guda biyu a yankin Naija Delta.

BBC ta ga wata wasika daga kamfanin Shell din inda kamfanin ya amince da daukar nauyin wannan kwarar mai.

Lauyoyin mutanen garin Bodo, wadanda ke zaune a cikin surkuki wanda ke malale da danyen mai sun ce wannan batu zai jawowa kamfanin mai na Shell biyan diyya ta miliyoyin daloli.

Lauyan mutanen garin na Bodo, Martyn Day ya ce wannan zai dasa dan-ba kan sauran kamfanonin da ke hakar mai a Birtaniya.