Malalar mai na barazana ga jama'ar yankin Ogoni

oil Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yankin Naija Delta a Najeriya

Za a shafe shekaru kusan 30 kafin yankin Ogoni da ke yankin Niger Delta a Najeriya ya farfado daga illar da malalar mai ya yi masa, a cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya.

Rahoton wanda aka dade ana tsammani ya ce gyara muhallin ka iya zamowa mafi "tsauri da kuma daukar lokaci a duniya" da aka taba yi.

Rahoton ya ce gurbatar muhalli na barazana ga lafiyar akalla al'ummomi 10 da ke yankin.

Tuni dai kamfanin mai na Shell ya dauki alhakin malalar mai biyu wacce ta lalata wasu al'ummomi a shekarun 2008 da 2009.

Daya daga cikin al'ummomin sun ce za su nemi a biya su diyyar daruruwan miliyoyi.

Shell ya ce zai sasanta kan batun a karkashin dokokin Najeriya.

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya, wanda aka shafe shekaru biyu ana yi, zai haifar da ce-ce-ku-ce saboda kamfanin Shell ne ya dauki nauyin gudanar da shi.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka fi hako danyan man fetur a duniya.

'Ba batun zargi bane'

Tun da farko Hukumar kula da Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (unep) ta gabatar da rahotonta ga shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

"Ba bincike bane da aka gudanar domin dora laifi kan wani kamfani da ke aiki a yankin Ogoni," a cewar mai magana da yawun Unep Nick Nuttall a hirarsa da BBC.

Image caption An dade ana rikici a yankin Ogoni

"Abin da muke fata shi ne na kawar da ce-ce-ku-ce wanda a wasu lokutan kan kai ga fada da tayar da hankali a shekaru da dama da suka wuce.

Ya kuma kara da cewa daukar alhakin malalar mai da Shell ta yi a wasu yankuna biyu ba shi da alaka da rahoton.

Martin Day, wani lauya da ke wakiltar mutanen Bodo a Ogoni, ya shaida wa BBC cewa yawancin yankin ya lalace sakamakon malalar mai.

"A sakamakon haka, kusan baki dayansu ba sa iya kamun kifi," a cewarsa. "An barsu ne kawai cikin matsanancin talauci."

'Za mu taimaka matuka'

Mr Day ya bayyana Shell a matsayin daya daga cikin kamfanonin da ya fi kowanne muni a duniya.

Sai dai a martanin da ya mayar, kamfanin na Shell ya ce ayyukan masu tayar da kayar baya ne ke haifar da yawancin malalar mai a yankin.

Manajin Daraktan kamfanin a Najeriya Mutiu Sunmonu, ya shaida wa kamafnin dillancin labarai na AFP cewa, rahoton Unep zai taimaka matuka wajen shawo kan lamarin.

"Rahoton ya taimaka a kokarin da ake yi na gano ainahin batun malalar mai a yankin Ogoni," a cewarsa.

"Za mu taimaka matuka wajen share man da ya malala".

Karin bayani