Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Illar cutar Polio ga yara

Image caption Matsalar Polio ta haifar da ce-ce-ku-ce a Arewacin Najeriya

Asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce shan inna wato poliomyelitis, cuta ce da ke kama jijiyoyin jikin dan adam kuma ta fi kama yara 'yan kasa da shekaru biyar.

Sai dai idan an yi rigakafi a kan iya kaucewa kamuwa daga cutar.

Haka kuma daya cikin yara 200 zuwa dari hudu da suka kamu da cutar na gamuwa da nakasa ko ma cutar ta yi ajalinsa.

A shekarar 1998 ne aka kaddamar da wani shiri na hadin guiwa kan kawar da cutar shan inna a fadin duniya.

Asusun UNICEF da Hukumar Lafiya ta duniya da kungiyar agaji ta Rotary International da kuma Cibiyar kariya daga kamuwa da cututtuka da kuma yaki da su ta Amurka sun fara wannan shiri don taimakawa gwamnatoci yaki da cutar shan inna a fadin duniya baki daya.

A cewar Asusun, tun lokacin da aka kaddamar da wannan shirin yara miliyan biyar ne suka samu kaucewa kamuwa daga cutar da ka iya kaisu ga nakasa ko ma ajali.

UNICEF ya ce kamuwa da wannan cutar da ake samu duk shekara ya ragu da kashi 99 cikin dari cikin dari wato daga dubu 350 a shekarar 1988 zuwa dubu daya da dari shida da shida a shekarar 2009.

Wannan nasara dai an alakanta ta ne da shirin digawa yara rigakafin kamuwa da cutar a kasashe.

Sai dai shirin hadin guiwar yace da sauran rina a kaba domin ya zuwa yanzu akwai kasashe hudu da wannan cuta ta yi katutu, kuma akwai wasu kasashe goma sha daya da suka kara kamuwa da cutar.

Asusun ya kuma ce har yanzu akwai sauran kalubalen da ke wa shirin kawar da cutar karan tsaye. Kuma sun hada ne da matukar yaduwar cutar a arewacin Indiya da matsalar tsaro a Afghanistan da arewacin Pakistan da kuma rashin yin ingantaccen aiki a arewacin Najeriya.

A shirin Haifi Ki Yaye na wannan makon, muna dauke da rahotanni kan illar wannan cuta: