Libya ta musanta rahoton kashe dan Gaddafi

Nato Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Nato na ci gaba da kai hare-hare a Libya

Gwamnatin Libya ta karyata rohotananin dake cewa an kashe daya daga cikin 'ya'yan kanar Gaddafi - Khamis Gaddafi a wani harin da sojin NATO suka kai.

Shi ne dai kuma komadan dakarun sojin kasar na musanman wadanda ke yaki yanzu haka a garin Zlitan.

Wani kakakin gwamntin Libya, Moussa Ibrahim ya ce Khamis Gaddafi na nan da ransa kuma babu abin da ya same shi.

Wannan dai shi ne karon na biyu a wannan shekarar da aka bada labarin cewa Khamis Gaddafi ya mutu.

Sai dai kakakin gwamnatin ya shaida wa 'yan jarida cewa harin da Nato ta kai ya yi barna matuka.

"Kunga abin da ya faru da idanunku, gawarwakin yara kanana da mahaifiyarsu, akwai misalai irin wadannan da dama a wasu sassan kasar."