Ra'ayi Riga : Batun wa'adin mulki guda a Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Batun wa'adin mulki guda na fiye da shekaru hudu, ga shugaban kasa da kuma gwamnoni a Nijeriya dai batu ne da zaa iya cewa ya sake janyo kace nace a 'yan kwanakin nan .

Tun bayan da wasu kafafen yada labarai suka tsegunta cewa shugaba Goodluck Jonathan na duba yiwuwar gabatar da shirin doka ga majalisar dokoki ta kasa, kan batun, a matsayin wani bangare na yi wa kundin tsarin mulki garambawul.

Wannan dai ba shi ne karon farko da batun ya taso ba, ko a zamanin gwamnatin Cif Olusegun Obasanjo an yi ta cece-kuce a kansa, daga bisani majalisar Dattawa ta yi watsi da shi a shekara ta 2007.

To ko wane alfanu ne ke tattare da wannan tsari na wa'adin mulki guda ga shugaban kasa ko gwamna, da wasu ke goyon bayan ganin an bullo da shi? Mene ne kuma nakasunsa da wasu ke adawa shi? Wasu kenan daga cikin abubuwan da zamu tattauna kansu a filinmu na ra'ayi Riga na yau.