Hannayen jari sun fadi warwas a duniya

stock
Image caption Damuwa akan faduwar hannayen jari a duniya

Darajar hannayen jari a kasuwannin hadahadar hannayaen jari a fadin duniya sun ci gaba da faduwa warwar, sakamakon shakkun da ake nunawa dangane da farfadowar tattalin arzikin duniya da kuma matsalar bashin da ta dabaibaye wasu kasashe masu amfani da kudin euro.

Tuni dai kasuwar hadahadar hannayen jari ta Japan ta fadi da fiye da kashi hudu cikin dari bayan 'yan mintunan kadan da bude ta.

Tun da farko dai kasuwar hadahadar hannayen jari ta Dow Jones da ke New York ta yi faduwa mafi muni a yini guda tun bayan koma bayan tattalin arzikin duniya shekaru uku da suka gabata.

Ministan kudi na Japan, Yoshihiko Noda, ya nuna damuwa a kan lamarin.

Yace "Wajibi ne mu ci gaba da mai da hanakali a kan darajar kudade, amma kuma yana da muhimmanci mu sa ido sosai a kan kasuwannin hadahadar hannayen jari bayan faduwar Dow Jones". Masu zuba jari da na fargabar cewa tattalin azrzikin Amurka ka iya fuskantar koma-baya, kuma mai yiwuwa matsalar karayar bashi a Turai ta yadu zuwa Italiya da Spaniya.