An amince da Yingluck a matsayin Firayi Minista

yingluck Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Sabuwar Firayi Ministar Thailand Yingluck Shinawatra

Majalisar Dokoki ta Thailand ta amince da mace ta firayim minista mace ta farko a kasar Yingluck Shinawatra, wacce jam'iyyar ta ta yi nasara da gagarumin rinjaye a babban zaben da aka gudanar a watan Yuli.

Mis Yingluck dai kanwa ce ga tsohon firayim minista Taksin Shinawatra, wanda ke gudun hijira tun bayan juyin mulkin da ya kifar da gwamnatinsa a shekarar 2006.

Yingluk Shinawatra ta samu goyon bayan kashi uku cikin biyar na 'yan majalisar wakilai ta kasar.

Sabuwar firayim ministar tana fuskantar kalubale da dama ciki har da magance rudanin siyasar da ya jawo rarrabuwar kawuna a kasar.

Tunani ya yawaita a Thailand cewar Mista Taksin na da hannu dumu-dumu a zabar ministoci, da kuma tsara manufofin sabuwar gwamnatin, al'amarinda shi da kanwar tasa suka musanta.