Amurka tsawaita takunkunmin ta ga Syria

clinton Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hilary Clinton

Amurka ta kara tsawaita takunkumin da ta kakabawa Syria, yayinda sojojin gwamnatin kasar ta syria ke ci gaba da yunkurinsu na murkushe masu zanga-zanga da karfi.

Takunkumin ya sahfi wasu fitattun 'yan kasuwa ne wadanda baitul malin Amurkan ya ce Shugaba Bashar al-Assad da dan uwansa na fakewa da su.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta ce Washington ta yi amanna gwamnatin ta Syria ce ke da alhakin kashe fiye da mutane dubu biyu tun bayan fara amfani da karfin soji watanni biyar da suka gabata.

Clinton tace "mun bi sahun Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya waje kira ga hukumomin Syria su dakatar da wadannan tashe-tashen hankula, su yi biyayya ga dokokin kasa-da-kasa, sanna su kyale ma'aikatan agaji na duniya su shiga kasar".

Ta kuma jaddada cewa Shugaba Assad ya sarayar da halacin mulkinsa.

A halin da ake ciki kuma masu fafutuka a Syrian sun ce sojoji sun kashe masu zanga-zanga hudu a kusa da birnin Damascus da kuma a kudancin kasar bayan sallar isha'i.