Dakarun Amruka talatin da daya sun mutu a Afghanistan

Sojan Amruka a Afghanistan Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Sojan Amruka a Afghanistan

Jami'an gwamnatin Afghanistan sun ce sojojin Amruka 31 da na Afghanistan 7 sun hallaka a wani hadarin jirgin helikofta a Gabashin kasar ta Afghanistan.

Wannan dai ita ce asarar rayUka mafi girma da Amruka ke yi a lokaci guda a Afghanistan din.

Al'ammarin dai ya faru ne a lardin Wardak a lardin Wardak.

Wani kakakin 'yan Taliban ya ce su suka harbo jirgin helikoftan, bayan da dakarun NATO suka kai hari a kan wani gida da masu tada kayar baya ke gudanar da wani taro.

Sai dai gwamnan lardin na Wardak, Halim Fedai ya ce har yanzu baa tantance musabbabin hadarin ba.