Babban Bankin Najeriya ya janye lasisin Bankuna uku

Image caption Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi

A Najeriya, gwamnatin kasar ta karbe bankuna guda uku, saboda fargabar cewa bankunan ba za su iya cimma wa'adin karfafa jarinsu da Babban Bankin kasar wato CBN ya kayyade kafin ranar 30 ga watan Satumba.

Bankuna dai sune Afribank da Bank PHB da kuma Spring Bank.

Babban bankin Najeriyar ya ce babu abunda zai shafi ajjiyar jama'a a bankunan, domin kuwa za'a maida ajiyansu ne a wasu bankuna na wucin gadi wadanda ake kira 'Bridge Banks' wanda Hukumar lura da ajiya ta kasar wato Nigeria Deposit Insurance Corporation ke tafiyar da su.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato, Karamin Ministan kudi na Najeriya, Alhaji Yerima Ngama na cewa Ma'aikatar kudin kasar na goyon bayan matakin karfe lasisin bankunan dari bisa dari da Hukumar lurra da ajiya ta kasar ta yi, na kafa bankunan wucin gadi, wato Bridge Banks domin warware matsalolin da bankunan Afribank da Bank PHB da kuma Spring Bank su ka shiga.

Masu ajiya

Ministan ya kara da cewa matakin da gwamnatin kasar ta dauka ba zai kawo matsala ga masu ajiya ba, domin anbi dukkan matakan da su ka dace domin kulla da ajiyarsu.

Shima dai babban Bankin Najeriya a wata sanarwa da ya fitar ya karfafa maganar cewa babu abun da zai samu ajiyar da masu hulda da bankunan su ka yi domin kuwa yana da kwarin gwiwa kan bankunan wucin gadin.

Bakunan wucin gadi wadanda ake kira 'bridge banks' sun hada da Enterprise Bank Limited da Keystone Bank Limited da kuma Mainstreet Bank Limited.

A shekarar dubu biyu da tara ne babban bankin Najeriya ya cire shugabannin wasu bankuna saboda yadda za suka gudanar da al'amuran bankin ba bisa tsari ba, al'amarin kuma da ya jefa bakuna cikin halin ni iyasu.

Karfafa jari

A wannan lokacin dai 'Babban Bankin' dai ya taimakawa bankunan wajen karfafa jarinsu.

Saboda wannan batun ne dai babban bankin ya sake diban wani sabon wa'adi wanda zai cika a ranar 30 ga watan Satumba ga bankunan domin su karfafa jarinsu.

Babban bankin dai ya ce an dau matakin soke lasisin wadanan bankunan ne saboda akwai shakkun cewa ba za su iya cimma wa'adin da aka dibar musu ba domin su karfafa jarinsu ba.