Hugo Chavez zai koma Cuba karbar magani

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hugo Chavez

Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez ya zai koma kasar Cuba a ranar asabar domin ci gaba da karbar maganin cutar sankara ko cancer da yake fama da ita.

Majalisar Dokokin kasar za ta gudanar da zama na musamman, don amincewa da tafiyar ta sa.

An cirewa Mr Chavez wani abu a kansa a kasar Cuba cikin watan Yuni, kuma tun lokacin yake karbar maganin cutar ta sankara.

Har yanzu dai babu wani bayani game da ainihin nauin cutar da yake fama da ita.

Rashin lafiyar ta sa ta sanya kokwanton cewa, anya kuwa zai iya tsayawa takarar zaben kasar da aka shiya yi badi.