Ministocin kudi na tattaunawa kan matsalar basussukan Turai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar Italiya na fama da matsalar bashi

Ministocin kudi da mahukuntan manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki, sun shiga wata tattaunawa ta gaggawa a wayar tarho, don binciko hanyar magance matsalar basussukan kasashen Turai.

Su na sa ran fiddo da sabbin matakai masu gamsarwa, kafin sake bude kasuwar hannayen jari a gobe litinin.

Babban bankin tarayyar turai, shima zai yi wani zama na musamman game da, ko zai sai basussukan kasar Italiya, wadda ita ce kasa mai karfin tattalin da matsalar ta shafa a baya bayan nan.

Duk dai dai masu hulda ba manyan bankuna an duniya sun nuna matukar damuwa game da rage matsayin Amurka wajen biyan basusukan da ake binta, abun da ya fi ci musu tuwo a kwarya a yanzu shine yadda suke kallon matsalar bashi a kasar Italiya ke ciki.

A yanzu haka dai kasar Italiya sai ta karbi wasu basusukan kafin ta iya sauke nauyin bashin da ake binta.

Masu ruwa da tsaki dai na ganin Babban Bankin Turai ne kawai zai iya karawa mutane kwarin gwiwa kan matsalar tattalin arziki da Italiya ta shiga.

Manyan Bankuna da masu sanya hannu jari a Turai na kokarin ganin Babban bankin ya saye wasu daga cikin bashin da ake bin kasar Italiya kamar yadda ta sayi na kasashen Ireland da Portugal da kuma Girka.

Idan har Babban bankin bai iya siyan bashin ba a ranar litinin akwai yiwuwar cewa za'a fuskanci matsala a kasuwanni hanayen jari a Turai.

Wannan kuma na nuni da cewa taron gaggawa da hukumar gudanarwa ta Bankin ta kira zai zai nuna alkiblar d tattalin arzikin Turai ta fuskanta, saboda ba dukan membobin hukumar bane ke goyon bayan siyan bashin na kasar Italiya.