An gudanar da zanga zangar tsadar rayuwa a Isra'ila

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wajen mutane dubu biyu ne dai su ka fito zanga zanga

Isra'ila ta fuskanci daya daga cikin zanga zanga mafi girma a tarihin kasar.

'Yan sanda sun ce, a kalla 'yan Isra'ila dubu dari biyu da hamsin, wadanda yawancinsu masu rufin asiri ne suka shiga zanga zangar, don nuna fushinsu game da tsadar rayuwa.

Zanga zanga mafi girma ita ce wadda aka yi a Tel Aviv, inda masu zanga zangar suka yi ta kururuwar cewa.

Masu zanga zangar sun ce dai alumma na gaba da kazamar riba.

Zanga-zangar wadda aka gudanar a ranar ita ce ta ukku da aka gudanar.

Wakilin BBC a birnin Qudus yace tashin farashin gidaje da kula da yara, da kayan abinci, ya batawa 'yan Isra'ilar da dama rai.