'Yan tawaye sun kaddamar da sabon farmaki a Libya

'Yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto none
Image caption 'Yan tawayen Libya

'Yan tawaye a Libya sun kaddamar da wani sabon farmaki a Yammacin kasar.

Bayan sun yi wani mummunan dauki ba dadi da sojojin dake biyaya ga Kanar Gaddafi, ga alama yanzu 'yan tawayen sun kama garin Bir Ghanem, wanda ke da nisan kilomita 80 daga Tripoli, babban birnin kasar.

Wannan dai shi ne karon farko da 'yan tawayen ke dannowa kusa sosai da birnin na Tripoli, kodayeke, babu tabbas idan za su iya cigaba da rike garin.

Yanzu dai 'yan tawayen sun ce suna shirin dannawa zuwa garin Zawiya na gabar teku, wanda suka taba kamawa a farkon yakin, amma daga bayan sojojin gwamnati suka kore su.