Sojoji sun harbe karamar yarinya a Maiduguri

Jami'in tsaro a Nijeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'in tsaro a Nijeriya

A Nijeriya takaddama ta barke tsakanin mazauna unguwar Budum dake tsakiyar birnin Maiduguri da kuma jami'an Rundunar samar da Tsaro ta JTF.

Jami'an rundunar tsaron sun yi harbin kan mai-uwa-da-wabi ne da yayi sanadiyyar rasuwar wata karamar yarinya mai kimanin shekaru tara da haihuwa.

Lamarin ya faru ne lokacin da wasu kungiyoyi ke rarraba kayan agaji ga 'yan kasuwar ta Budum.

Rundunar tsaron ta JTF ta tabbatar da afkuwar lamarin,sai dai ta musanta zargin yin harbi da gangan.