Kananan hukumomi a Najeriya sun zargi al'umominsu da hana su aiki

Image caption Taswirar Najeriya

A tsari irin na dimokradiyya, daya daga cikin hanyoyinda shugabannin kan samu a zabe su, shine ta hanyar yi wa alummarsu alkawuran irin abubuwan alhairinda za su aiwatar idan aka zabe su.

To sai dai ba kasafai 'yan siyasar kan cika wadannan alkawura ba.

Sau tari dai, wa'adin shugabannin kan kare ba tare da sun samu aiwatar da mafi akasarin abubuwanda suka yi alkawari ba.

To sai dai masu iya magana na cewa, idan an bi ta barawo, to a bi ta mabi sawu, don kuwa wasu shugabannin, a Najeriya sun ce alummominsu ne ke hana su yin aiki.

A cikin fiye da shekaru 12 na mulki demokradiyya, jama'a da dama na ganin kananan hukumomin sun karbi mukudan kudade domin inganta rayuwar jama'arsu.

Sai dai al'ummomin da suke wakilta sun ce ba su aiwatar da ayyukan da su ka yi daidai da irin kudin da su ka samu ba.

Sun dai alakanta hakan ne da cin hanci da rashawa.

Sai da wasu shugabanin kananan hukumomi sun musanta hakan, idan suka ce, bukatun al'umarsu sun hana su isasun kudaden gudanar da manyan ayyuka.

Sun ce a ko da yaushe jama'a da dama sun na binsu ne domin maula.