An gudanar da addu'o'in rokon ruwa a Nijer

Shugaba Muhammadou Issoufou
Image caption Shugaba Muhammadou Issoufou

A Jamhuriyar Nijar an gudanar da wasu addu'o'i na rokon ruwan sama a birnin Yamai.

Hakan dai ya biyo bayan kiran da hukumomin kasar suka yi ne na a gudanar da irin wadannan addu'o'i a duk fadin kasar, saboda matsalar karancin ruwan da ake fama da ita a wasu yankuna karkara na kasar.

Shugaban kasar ta Nijar, Alhaji Mahamadou Issoufu da Firaminista, Alhaji Birji Rafini, duka sun halarcin taron addu'o'in na yau da safe, da aka gudanar a babban masallacin Jumaa, cikin wani yanayin ruwan sama.