Hukumar kididdigar bashi ta rage matsayin Amurka

Image caption Shugaban Amurka, Barrack Obama

Hukumar kididdigar matsayin karbar bashi ta Standard and Poor's, a karon farko ta rage matsayin Amurka na iya biyan basussuka da mataki guda.

Hukumar dai ta rage matsayin Amurka ne daga matsayi mai daraja ta ukku, ta koma matsayi mai daraja ta biyu.

Wannan rage matsayi dai wata babbar komabaya ce ga harkar tattalin arzikin kasar.

Hukumar a wata sanarwa da ta fitar ta ce yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin Amurka da 'Yan majalisar kasar game da rage irin basusukan da ake bin ta bai yi tasiri ba.

Har wa yau Gwamnatin Amurka ta karyata rahoton Hukumar ta Standard and Poors, inda ta ce hukumar tayi babbar kuskure wajen hada kididigar ta.

Gwamnatin Amurka ta ce akwai wajen gibin dala trillion biyu na kudin kasar da hukumar ba ta yi la'akari da su ba wajen kididigar da tayi kafin ta wallafa rahoton ta.

A yanzu haka dai bashin da ake bin kasar Amurka ya kai sama da dala trillion goma sha hudu.