Kungiyar hadin kan Larabawa ta yiwa Syria kashedi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban kungiyar hadin kan Larabawa, Nabil Al-Araby

Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta yi kira ga gwamnatin Syria da ta daina murkushe masu zanga-zanga nan take. A wata sanarwa da ta bayar, wadda ita ce mafi karfi tun bayan da aka fara boren neman kawo sauyi a kasar ta Syria, kungiyar ta ce tana nuna matukar damuwa game da yadda yanayin tsaro ya tabarbarwe a kasar. Wakilin BBC ya ce kafin ta fitar da wannan matsayi, akwai rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen Kungiyar dangane da batun Syria. Amma sanarwar ta yau, wata alama ce ta irin karin matsin lambar da gwamnatin Syriar ke fuskanta daga kasashen duniya. Firaministan Turkiyya, Recep Tayyib Erdohan, ya ce kasarsa, wadda ke makwabtaka da Syriar, ta gaji da yin hakuri. An shirya a ranar Talata mai zuwa ne Ministan harkokin wajen Turkiyyar zai je birnin Damasucus dauke da wani sauko mai tsauri ga hukumomin kasar.