Bankunan da aka kwacewa lasisi a Nijeriya sun sami Shugabanni

Image caption Sanusi Lamido, Gwamnan babban bankin Nijeriya

Yayinda babban bankin Nijeriya, CBN ya kwace lasisin bankunan Afribank da Spring Bank da PHB, tuni kamfanin sayen basussukan da aka kasa biya na kasa, wato AMCON ya bayyana sunayen sababbin hukumomin da zasu gudanar da wadannan bankuna. Bankunan wadanda yanzu za a kira su da sunayen Keystone Bank, da Mainstreet Bank, da kuma Enterprise Bank, zasu kasance ne a karkashin jagorancin Mr Jacobs Moyo Ajekigbe, da Malam Falalu Bello, da kuma Mr Emeka On-wuka. Sai dai abin tambaya anan shi ne wane irin kalubale ne ke gaban wadannan sabababbin shugabanni, na tabbatar da cewa wadannan bankuna sun mike? Malam Abubakar Aliyu, wani masanin tattalin arziki ne a Abuja, kuma ya shaidawa BBC cewa, sababbin shugabbanin zasu yi kokarin inganta jarin bankuna domin su tsaya da kafafunsu.