Sojojin Syria sun kai karin hare-hare a garuruwa biyu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Syria

'Yan adawa a Syria sun ce sojojin gwamnati sun kai hari a kan wasu garuruwa biyu, tare da kashe mutane fiye da 50, cikinsu har da wani yaro mai shekaru 10. Sun ce akalla mutane 38 ne aka kashe, lokacin da sojojin suka afka wa birnin Deir Ezzor dake Arewa maso Gabashin kasar, suna ta harbi akan masu zanga-zanga. 'Yan adawan dai sun gudanar da wasu jerin zanga-zangar nuna kyamar gwamnati a birnin na Deir Ezzor tun lokacin da aka fara bore a kasar ta Syria a cikin watan Maris, amma yanzu rahotanni sun ce yankunan kasar da dama suna karkashin ikon gwamnati ne. Har illa yau 'yan adawar sun ce an kashe mutane 12 a garin Hula, kusa da birnin da Homs, bayan da sojoji tare da tankokin yaki, suka kai hari akan garin da Asubahi.