Kungiyar G7 na neman mafita kan matsalar tattalin arziki

Image caption Taron Ministocin kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki

Kungiyar kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki sun ce, za su dauki dukkanin matakan da suka wajaba, don tabbatar da cewa an samu daidaito a harkokin tattalin arzikin duniya.

Sun dauki wannan mataki ne, sailin da harkar tattalin arzikin kasashen Turai da Amurka suka shiga rudu sakamakon tsananin basussukan da suka yi masu katutu.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, kungiyar ta ce tana kokarin daidaita al'amura ne a kasuwar hadadar hannayen jari bayan hanayen jari sun fadi warwas a makon daya gabata.

Har wa yau dai hannu jari na Nikkei a kasar Japan ya yi kasa da kashi daya cikin dari bayan an bude kasuwar hanayen jari a kasar a yau din nan.

Tun farko dai Babban bankin Turai ya bayana cewa zai sayi kaddarorin gwamnati na Bonds daga kasashen Turan dake fama da matsalar bashi, musamman ma kasar Italiya da Spain.

Asusun bada lamuni na duniya ya ce matakin da kasashen G-7 din suka dauka da na Babban bankin Turai zai taimaka gaya wajen kara kwarin gwiwa da kuma inganta tattalin arziki.