Farashin hannayen jari na ci gaba da faduwa a duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasar Amurka ta kara kwarin gwiwa wajen biyan ba basusukan da ake binta

Farashin hannayen jari a kasuwannin nahiyar Asia sun sake faduwa a yayinda manyan kasashen duniya ke fama da matsalar tattalin arziki.

Hakan ya auku ne duk kuwa da jawabin da shugaba Obama yayi na shawo kan masu zuba hannayen jari a kasuwannin duniya cewa Amurka na daukar matsalolin basussukanta da muhimmanci.

Shugaba Obama dai ya ce Amurka za ta yunkura don shawo kan matsalolin tattalin arziki da fada ciki.

Kafin rana ta kai tsakiya, hannayen jari a Hong Kong sun fadi da kashi shidda cikin dari.

Haka zance ma ya ke a Tokyo inda suka fadi da kashi hudu.

Saidai darektan dandalin hada hadar hannayen jari ta Dow Jones a Amurka Alan Valdez ya ce abin bai zo ma su da mamaki ba.

Ya ce; "Idan ka dubi yadda aka rufe kasuwannin, ta yiwu a gobe a sake samun masu neman siyar da hannayen jarinsu," In ji Alan Valdez